Romans 10

1ʼYanʼuwa, abin da zuciyata take so da kuma adduʼata ga Allah saboda Israʼilawa shi ne su sami ceto. 2Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba. 3Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah. 4Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya.

5Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa: “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”
L Fir 18.5
6Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa: “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’
M Sh 30.13
” (wato, don yǎ sauko da Kiristi),
7“ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’ ” (Wato, don yǎ hauro da Kiristi daga matattu). 8Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,”
M Sh 30.14
wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela:
9Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya ta da shi daga matattu, za ka sami ceto. 10Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka. 11Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.”
Ish 28.16
12Gama ba bambanci tsakanin Bayahude da Baʼalʼumme-Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi, 13gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”
Yow 2.32


14To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu waʼazi ba? 15Kuma ta yaya za su yi waʼazi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”
Ish 52.7


16Amma ba dukan Israʼilawa ne suka karɓi labari mai daɗin nan ba. Gama Ishaya ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu?”
Ish 53.1
17Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi. 18Amma ina da tambaya: “Ba su ji ba ne? Hakika sun ji:

“Muryarsu ta tafi koʼina a cikin duniya,
kalmominsu kuma har iyakar duniya.”
Zab 19.4

19Har wa yau, ina da tambaya: Shin, Israʼila ba su fahimta ba ne? Da farko, Musa ya ce,

“Zan sa ku yi kishin waɗanda ba alʼumma ba;
zan sa ku yi fushin alʼummar da ba ta da fahimta.”
M Sh 32.21

20Ishaya kuma ya fito gabagaɗi ya ce,

“Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni;
Na bayyana kaina ga waɗanda ba su ma taɓa neman sanina ba.”
21Amma game da Israʼila ya ce,

“Dukan yini na miƙa hannuwana
ga mutane marasa biyayya da masu taurin kai.”
Ish 65.2

Copyright information for HauSRK